Shugaban Amurka Donald Trump ya fadawa shugabannin Afrika cewa zai tura jakadiyar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya, Nikki Haley zuwa Sudan ta kudu da janhuriyar Dimokradiyyar Congo.
A wata liyafar cin abinci, inda Trump ya gana da shugabannin Afrika a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya yau Laraba, shugaban ya ce, “Amurka na sa ido sosai kuma ta damu matuka akan tashin hankalin dake faruwa a Sudan ta kudu da Congo. Ya kuma ce, miliyoyin rayuka na tattare da hadari kuma Amurka na cigaba da bada taimakon jinkai, amma tabbataciyyar hanyar kawo karshen wannan bala’in zata bukaci shirin samar da zaman lafiya karkashin jagorancin shugabannin Afrika, da kuma sa hannun duka bangarori.
Trump ya kuma ce Haley zata tattauna akan hanyoyin warware rikici da kuma muhimmin abu, kaucewa rikicin kansa. Sudan ta kudu ta sami kanta cikin yakin basasa shekaru 4 kenan, wanda ya tilastawa mutane kusan miliyan 4 yin gudun hijira, yayinda Congo kuma ke fuskantar karin tashe tashen hankali sanadiyar rikicin kabilanci da kuma rashin tabbas din ko yaushe kasar zata gudanar da babban zaben shugaban kasa.
Shugaban Congo Joseph Kabila ya kasance a kan karagar mulki fiye da wa’adin mulkinsa wanda ya kare a shekarar 2016.