Masu gabatar da jawabai da mambobin kwamitin a taron zasu kunshi manyan jami’an farar hula da na soja, a cewar Laftanar Kanal Bobby Dixon, mai magana da yawun rundunar sojin Amurka a Afirka da ake kira AFRICOM.
Dixon ya ce, "Manufar taron ita ce tunkarar kalubalen tsaro a nahiyar Afirka da kuma gano hanyoyin aiki tare don samar da tsaro da kariya a Afirka. Kama daga kokarin yaki da ta'addanci zuwa barazanar kutsen yanar gizo da ayyukan wanzar da zaman lafiya, taron zai tattauna a kansu duka.
Rundunar AFRICOM ta ce taron zai dora kan nasarorin da aka samu a tarukan baya. Taron da aka yi a shekarar da ta wuce a birnin Rome na kasar Italiya, ya samu mahalarta mafi yawa, inda kasashe 43 suka tattaru.
Ku Duba Wannan Ma Najeriya Na So Amurka Ta Mayar Da Rundunar Sojin AFRICOM Zuwa AfirkaBayan taron kili kan harkokin tsaro da aka yi a watan Maris, Kungiyar Tarayyar Afrika ta bayyana matukar damuwa kan karin tashin hankali da ake fuskanta a nahiyar da kuma tasirin shi ga ci gaban nahiyar da zamantakewar al'umma.