WASHINGTON, D.C —
Hukumar Sararin samaniyar Amurka NASA, ta shirya harba wani makami zuwa tashar sararin samaniyar kasa-da-kasa daga kasar Amurka, karon farko tun daga shekara ta 2011.
‘Yan sama jannati 2 na hukumar ta NASA ne za su kasance a cikin kumbon da zai tuka makamin, wanda shine mataki na karshe na gwajin aikin na NASA tare da wasu kamfanonin masu zaman kan su, na dawo da tura Amurkawa a sararin samaniya.
Tun sa’adda aka dakatar da ayyukan harba kumbo, hukumar NASA tana dogara ne ga hadin gwiwa da hukumar sararin samaniya ta kasar Rasha, domin aikewa da ‘yan sama jannatin Amurka zuwa ISS.
Ana sa ran shugaban Amurka Donald Trump da mataimakinsa Mike Pence su halarci cibiyar tunawa da Kennedy a Florida, inda za’a harba kumbon a yau Laraba.