Yau Litinin ce ranar tunawa da ‘yan mazan jiya a Amurka, ranar da aka ware don tunawa da dubban dakarun Amurka maza da mata, da suka sadaukar da rayuwar su ga kasar.
An sassauta Tutocin kasar zuwa rabi a duk fadin kasar don karrama su a yau Litinin, bisa umarnin shugaba Donald Trump, an kuma saukar da tutocin tun daga ranar Juma’a har zuwa jiya Lahadi, da zummar girmama Amurkawa fiye da mutum 100,000 da suka mutu a sandiyyar annobar coronavirus.
Mace-macen Amurka wanda ya zarce na kowace kasa a Duniya, sun hada da tsofaffin sojoji 1,000 da suka mutu saboda COVID-19, a cewar ma’aikatar lamurran tsofaffin sojoji.
Hutun ya yi dai-dai da lokacin fara hutun bazara a Amurka, to amma tare da dokokin ba da tazara, da takaita shigowar matafiya daga kasashen waje da kuma miliyoyin mutane da suka rasa ayyukan yi, wannan lokacin zai banbanta da na shekarun da suka gabata.
Trump ya tsara gudanar da bikin saka fulawa a makabartar tunawa da mazan jiya ta Arlington, kana zai kuma kwashe wani lokaci na bikin ranar, a Fort MCHenry da ke Baltimore, inda aka yi wani yakin basasa na shekarar 1812 mai dunbin tarihi.
Magajin Garin Baltimore Jack Young, ya roki shugaba Trump da kada ya zo garin nasu, yana mai cewa hakan ya sabawa sakon hana ‘yan Baltimore yin tafiya zuwa wani guri da ya bayar. Trump ya ki amfani da kyallen rufe hanci a cikin jama’a, akan haka Young ya ce, ba sa bukatar ziyarar ta Trump.
Facebook Forum