A yau Talata a ke sa ran Amurka za ta fitar da sabuwar dokar hana ‘yan kasar Brazil shigowa, kwanaki biyu kafin ranar da fadar White House ta shirya sanarwar, a kokarin dakile yaduwar coronavirus. Hukumomi basu bada dalilan yin hakan ba gabanin sanarwar da aka shirya yi a ranar Alhamis.
Dokar ta shafi bakin da za su shigo kasar da suka ziyarci Brazil a cikin kwanaki 14. Jami’an kiwon lafiya sun ce, yakan dauki kwanaki 2 zuwa 14 kafin alamomin kwayar cutar COVID -19 ta bayyana a jikin wanda yake dauke da ita.
Kididdigar Jami’ar Johns Hopkins ta nuna cewa Brazil ta zamo kasar da cutar ta yi kamari a kwanakin nan, wadda kasar Amurka ce kadai ke gabanta da yawan wadanda suka kamu da cutar.
Ma’aikatar lafiyar kasar Brazil ta sanar a jiya Litinin cewa cutar tayi sanadiyar mutuwar mutane 807 a cikin sa’oi 24, yayin da adadin wadanda suka mutu a Amurka a kwana daya ya kai 620.
Fadar ta White House ta ce dokar za ta tabbatar da ganin baki basu yi sanadin samun sabbin masu kamuwa da cutar ba a kasar. Tuni shugaban Amurka Donald Trump ya kakaba irin wannan doka akan kasashe kamar China, Iran, Ingila, Ireland da kuma kasashe 26 dake nahiyar Turai.
Shugaban Kasar Brazil Jair Bolsonaro ya dade ya na boye tsananin illar da cutar coronavirus ta yi wa kasar tsawon watanni, inda ya ba da damar ci gaba da gudanar da kasuwanci da kuma janye dokokin ba da tazara a tsakanin jama'a.
Facebook Forum