A yau Litinin Amurka za ta bude sabon ofishin jakadancinta da ke Birnin Qudus, inda ta ce za ta hade daukacin ayyukan diplomasiyyanta a sabon ofishin jakadancin.
Wata sanarwa da ma’aikatar harkokokin wajen Amurka ta fitar a jiya Lahadi , ta ce, matakin ba ya nufin Amurka za ta sauya manufofinta ba ne a Birnin Qudus, ko yankin Yammacin Gabar Kogin Jordan ko na Zirin Gaza.
Sanarwar ta kara da cewa, matakin, kokari ne na inganta ayyunkan diplomasiyan Amurka da aikace-aikacenta a yankin.
Falasdinawa na adawa da wannan mataki na Amurka, domin a cewarsu, dauke ofishin jakadancin daga Tel Aviv zuwa Birnin Qudus, na nuni da cewa Qudus ya zama babban birnin Isra’ila.
A watan Oktoban bara, Sakataren harkokin wajen Amurka, Mike Pompeo, ya bayyana cewa Amurka za ta mayar da ofishin jakadancinta zuwa Qudus.