Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Da China Na Gab Da Cimma Yarjejeniyar Ciniki


Shugaban China Xi da takwararsa na Amurka Trump
Shugaban China Xi da takwararsa na Amurka Trump

Manyan jami’an dake tattaunawa akan batun cinikayya na Amurka sun fada a jiya Laraba cewa ba a ko kusa da cimma yarjejeniyar kasuwanci da kasar China ba.

“Akwai abubuwa da dama da yakamata a yi kafin a kai ga kulla yarjejeniyar,” inji wakilin Amurka a kan harkokin cinikayya Robert Lightizer, yayin da yake bada bahasi a gaban wani kwamiti na majalisar tarayya a nan Washington. Ya kuma ce “Idan muka kai ga kammala wadannan abubuwan, wato in har, kuma idan muka iya cimma kuduri akan batun aiwatarwa, to ta yiwu mu cimma yarjejeniyar da zata bamu damar warware takardamarmu, mu kuma inganta alakar dake tsakani mu da kasar China.

Amurka da China, kasashe biyu da suka fi karfin tattalin arziki a duniya, sun kwashe watanni suna tattaunawa a kan cimma sabuwar yarjejeniyar kasuwanci, duk da cewa sun yiwa juna karin haraji mai yawa akan kayayyakin da suke saidawa juna na biliyoyin daloli.

Lightizer yace wakilan kasashen biyu dake tattanawa a nan Washington da birnin Beijing suna samun ci gaba sosai.

Shugaba Donald Trump ya ambaci ci gaban da aka samu ranar Lahadi, na dage matakin karin haraji akan kayayyakin kasashen biyu wanda da gobe Jumma’a matakin zai fara aiki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG