WASHINGTON, D. C. - Amurka za ta aika wa Ukraine makami mai linzami na Patriot, a cewar wasu jami'an Amurka biyu ranar Talata, a matsayin maida martani ga kiraye-kirayen da Kyiv ta yi na neman taimakon gaggawa wajen samun karin na’urorin kariya ta sama yayin da kasar ke fama da hare-haren Rasha a yankin Kharkiv.
Wannan zai zama makami mai linzami samfarin Patriot na biyu da Amurka ta bai wa Ukraine, ko da yake ma’aikatar tsaron Pentagon ta tura makamai masu linzami da ba a bayyana adadinsu ba. Sauran kasashen kawancen Ukraine da suka hada da Jamus, su ma sun sama wa Ukraine da na'urorin kariya ta sama da kuma alburusai.
Jami’an na Amurka biyu sun yi magana ne bisa sharadin a sakaya sunayensu saboda ba a sanar da matakin ba. Jaridar New York Times ce ta fara ba da rahoton matakin.
A karshen watan da ya gabata, shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskyy ya nemi karin makami mai linzamin Patriot na Amurka, yana mai cewa makaman zasu taimaka wa dakarunsa wajen kakkabo bama-bamai kusan 3,000 da Rasha ke harbawa cikin kasar duk wata.
Da yake magana a Madrid, Zelenskyy ya ce har yanzu Ukraine na bukatar karin wasu makaman guda bakwai don dakile hare-haren da Rasha ke kai wa kan manyan na’urorin samar da wutar lantarki da yankunan farar hula, da kuma wuraren soja.
Ya ce Ukraine na bukatar biyu daga cikin makaman don kare Kharkiv, inda Rasha ta kaddamar da hare-haren tsallaken iyaka a ranar 10 ga watan Mayu, lamarin da ya sa har yanzu sojojin Ukraine ke gwagwarmaya.
"Idan muna da waɗannan makaman na Patriot na zamani, jiragen sama na Rasha ba za su iya zuwa kusa su jefa bama-bamai a kan farar hula da sojoji ba," in ji Zelenskyy a wani taron manema labarai a babban birnin Spain.
-AP