Bikin na ranar hudu ga watan Yuli, biki ne kuma na tabbatar da zama dan kasar Amurka. Amurkawa a ko’ina su ke a duniya suna daukar wannan rana da muhimmancin gaske da gudanar da shagulgula iri dabam dabam da ke nunawa da kuma jaddada so, da kishin kasa.
Your browser doesn’t support HTML5
An gudanar da bikin a sassan Amurka da baje wasan wuta da ya rika tartsatsi da haske a birane da garuruwa, manya da kanana. An kuma yi faretin murnar democradiyyar kasar a ko ina a fadin Amurka, da jadada 'yancin fadin albarkacin baki, 'yanci kada kuri’a, ko akasin haka, da kuma 'yancin yin addini ko akasin haka.
Tun da farar safiyar Alhamis da ga ko ina suka hallara a farfajiyar ginin Majalisa Capitol Hill domin gane wa idanun su irin kayataccen bukin da aka gudanar a wurin, da ya hada da fareti, harba bindiga, kade kade da raye raye da wake waken shahararrun mawakan kasar, da wasan wuta mai dauke da launuka iri dabam dabam da ya rika haske sararin samaniya.
Your browser doesn’t support HTML5
Kimanin mutane dubu goma sha daya su ka zama 'yan kasar Amurka a hukumance a makon da ake hutun gudanar da shagulgulan, adadin da ya ninka akan na shekara guda ta da wuce. Hukumar dan kasa ta Amurka da ta shigi da fici, ta shirya bukukuwan zama dan kasa har dari da casa’in da biyar a sassan duniya, tsakanin 28 ga watan Yuni da 5 ga watan Yuli.