Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Tarayyar Najeriya Ta Ci Gyaran Rahoton NYT


The NYT
The NYT

Fadar Gwamnatin Najeriya ta ce ba a yi mata adalci ba a rahoton da mujallar New York Times ta wallafa da ya jibinci tattalin arziki da tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar.

Da yake maida martani kan rahoton, mai ba Shugaban Najeriya Bola Tinubu shawara na mussamman kan harkokin sadarwa da tsare tsare, Bayo Onanuga yace, baya ga cewa, gwamnatin Shugaba Tinubu ta gaji matsalar daga gwamnatin da ta gabata, ya dauki kwararan matakai na rage radadin tsadar rayuwar da hawan shi mulki, da su ka taimaka, su ka kuma fara magance dalilan da su ka janyo tsadar rayuwar.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)
Shugaba Bola Ahmed Tinubu (Facebook/Asiwaju Bola Ahmed Tinubu)

Mashawarcin na musamman ya ce, mujallar ta dora alhakin matsanancin halin kunci da ake fuskanta a kasar, ta yin la'akari da bayanan wadanda ta yi hira da su da suka bayyana irin halin kuncin rayuwa da su ka fuskanta cikin shekara guda da ta shige, kan gwamnatin Shugaba Tinubu ba tare da la’akari da ci gaban da aka samu a fannin tattalin arziki karkashin mulkin sa ba, duk kuwa da cewa, Tinubu ya gaji wadannan matsalolin ne.

Yace ya zama wajibi gwamnati ta maida martani kan rahoton domin fayyace gaskiyar lamarin, da kuma matakan da gwamnati Bola Tinubun ke dauka na shawo kan lamarin, domin inganta rayuwar al’umma da ya hada da janye tallafin man fetur da ya ke hana gwamnatin sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.

Food Items on Display at a Market in Garki Area 11
Food Items on Display at a Market in Garki Area 11

Onanuga ya bayyana cewa, Najeriya ta shafe shekaru da dama tana aiwatar da tsarin tallafin man fetur da ya lakume sama da dala biliyan 84.39 tsakanin shekarar 2005 zuwa 2022 daga baitul malin gwamnatin kasar, da ke da nakasu wajen samar da ababen more rayuwa, abinda kuma ya ke hana gwamnati iya samar da ayyukan inganta rayuwar al'umma..

Bisa ga cewar shi, ana bin kamfanin mai na NNPC tiriliyan na naira saboda rashin biyan kudin tallafin.

ABUJA: NNPC
ABUJA: NNPC

Mai ba Shugaban kasar shawara na musamman ya kuma yi karin haske kan kokarin da gwamnatin Tinubu ta ke yi na shawo kan hauhawar farashin kayayyaki, musamman hauhawar farashin kayayyakin abinci, ta hanyar kara bunkasa ayyukan noma, da tsare-tsare da jihohi suka yi na sayar da abinci a farashi mai rahusa.

Onanuga ya ce, ba Najeriya kadai ke fama da tsadar rayuwa ba, amma har a kasar Amurka da sauran kasashen duniya ana fama da tsadar rayuwa da ke shafar rayuwar al'umma ta yau da kullum a kasashen.

Mujallar New York Times ta wallafa rahoto a ranar 11 ga watan nan na Yuni kan kalubalen tattalin arzikin da ‘yan Najeriya ke fuskanta sakamakon hauhawar farashin kayayyaki da aka fara fuskanta a shekarar da ta gabata da ya ci gaba da tsananta, ta kuma alakanta matsalolin da manufofi da tsare-tsaren gwamnatin Tinubu.

Zanga-zangar tsadar rayuwa da NLC ta gudanar
Zanga-zangar tsadar rayuwa da NLC ta gudanar

Makonni biyu da su ka gabata, manyan kungiyoyin kwadago na Najeriya su ka shiga yajin aiki da nufin neman karin albashi bisa la'akari da tsadar rayuwa da ake fuskanta a kasar da masu kula da lamura ke danganta wa da janye tallafin man fetur, da kuma faduwar darajar Naira. Wannan yajin aikin shi ne na hudu da kungiyar kwadagon ta shiga a cikin shekara guda da kafa gwamnatin Tinubu.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG