Amurka Tayi Allah Wadai Da Gallazawa Mata A Masar

Gungun matan Misra d a suka yi zanga zangar yadda jami'an tsaro suke cin zarafin mata.

Dakarun tsaron kasar Masar sun yi arangama da masu zanga zanga a dandalin Tahrir dake birnin alkahira a ci gaba da yunkurin tarwatsa wadanda ke kira ga majalisar mulkin soja ta ajiye mulki.

Dakarun tsaron kasar Masar sun yi arangama da masu zanga zanga a dandalin Tahrir dake birnin alkahira a ci gaba da yunkurin tarwatsa wadanda ke kira ga majalisar mulkin soja ta ajiye mulki.

Yansan da sojoji sun kai sumame a dandali yau Talata da asuba da zumar korar jama’a daga tsakiya birnin inda aka yi zanga zangar da ta yi sanadin hambare gwamnatin shugaba Hosni Mubarak.

Masu zanga zanga da jami’ar tsaro sun rika jifar juna da duwatsu, yayinda ‘yan sanda suka suka yi harbe hare da nufin tarwatsa masu zanga znagar yayinda gumurzun ya shiga kwana na biyar.

A kalla mutane 12 aka kashe sama da dari biyar kuma suka jikkata tun daga ranar jumma’a.

Shugabannin mulkin sojan kasar Misira sun kare amfani da karfi da cewa masu zanga zangar sun takali sojoji suka kuma lalata kaddarorin gwamnati.

Sakatariya ma’aikatar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton ta bayyana a jawabinta jiya Litinin da dare cewa, abinda ya faru na baya bayan nan ya bada mamaki musamman yadda aka muzgunawa mata.

Aika Sharhinka