Amurka tana bukin zagayowar ranar samun yancin kai

Amurkawa na bukin cika shekaru 242 da samun yancin daga Birtaniya ne ta hanyar gudanar da liyafar zuwa wani fili ko gandu ayi gashe gashe a ci abinci tare da ake cewa picnic da turanci da gudanar da fareti da kuma shirya wasan wuta.


Shugaban Amurka Dnald Trump da uwargidansa sun shiryawa iyalan sojoji liyafa a fadarsa ta White House.


Bukukuwar ranar hudu ga wata Yulin zai hada ne da abinda aka saba yi bisa al’ada karanta ayyanar samun yanci a matakalar cibiyar adana kayan tarihi ta kasa a nan Washington. A cikin ginin kuma, za a baje muhimman takardu tare da kundin tsarin mulki kasar da kuma dokokin yanci domin jama’a su duba.


Jim kadan bayan jawabin ayyana samun yancin, dubban mutane zasu yi fareti a gaban ginin a kan titin Constitution kuma faretin zai mike zuwa yammacin ginin kuma yake tsakanin fadar White House da dandalin tunawa da shugaban Amurka na farko George Washington