Gwamnatin shugaba Donald Trump a nan Amurka ta bayyana tsarin kasar Rasha na bude kofar ayyukan jinkai domin kwashe fararen hula daga wata gunduma dake bayan garin birnin Damascus, a matsayin wata almara.
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Amurka, Heather nauert, ta ce, "abinda ya kamata ya faru shine a aiwatar da shirin tsagaita wuta a duk fadin kasar, kamar yadda Kwamitin Sulhun Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ya amince ba tare da hamayya ba a ranar Asabar da ta shige." Ta ce kasashe 15, tare da kasar Rasha sun amince da wannan kudurin.
Nauert tace a fili yake cewa shirin tsagaita wuta na tsawon kwanaki 30 a gabashin Ghouta da kwamitin sulhu na MDD ya amince dashi, ba ya aiki, tace ba wanda Amurka ke ganin laifin sa akan wannan illa Rasha wadda ta ci gaba da horas da da sojojin Syria tare da ba su makamai.
Akan haka ne Amurka ta yi kira ga Rasha da ta matsa wa kasar ta Syria ta daina wannan fadan a Ghouta, har ma da sauran wurare.
Rasha dai ce ta yi gaban kanta wajen bayyana dakatar da fada na tsawon sa'o'i 5 a kullum, a inda ‘yan tawaye suke rike dashi a gabashin Ghouta a ranar Litinin, ta yadda masu ayyukan jinkai zasu iya kaiwa ga fararen hula.
Sai dai ba wanda yayi anfani da wannan damar ta dakatar da fada na tsawon sa'o'in biyar, a bisa alamu domin ba su amince da Rasha ko kuma gwamnatin Syria ba, haka kuma babu wani kayan agaji da aka shiga da shi gundumar.