Amurka Tayi Kira Ga Turkiyya A Kan Yunkurin Juyin Mulkin Kasar Da Bai Yi Nasara ba

Amurka na kira ga kasar Turkiyya ta kai zuciya nesa kuma kar ta saba ma ka'ida, yayin da ta ke binciken yinkurin juyin mulkin makon da ya gabata da bai yi nasara ba, a daidai lokacin da ake samun rahotannin da ke cin karo da juna kan ko tsohon kwamandan sojojin sama ya amsa cewa shi ne madugun yinkurin juyin mulkin ko a'a.

Kafar labaran gwamnati ta 'Andolu' ta ce an dakatar da sojoji 8,777, kuma an tsare jami'an shari'a da kuma sojoji 6,000 bayan yinkurin juyin mulkin da aka yi a ranar Jumma'a, abin da ya tada hankalin Shugabannin kasashen duniya, har su ka yi kashedi kan daukar matakan da ka iya yin illa ga kundin tsarin mulkin kasar.
Jiya Litini, kafar labaran ta Andolu ta ambato Janar Akin Ozturk, wanda tun farko ya nesanta kansar daga boren da aka yi ma gwamnatin Shugaba Recep Tayyip Erdogan, wai yana cewa ya yi "yinkurin juyin mulki."

To amma tuni kafar labaran ta janye wannan rahoton kuma an karyata zargin cewa yana cikin sauran kafafen yada labaran Turkiyya wadanda ba na gwamnati ba.

A Brussels jiya Litini, Sakataren Harkokin Wajen Amurka John Kerry ya ce yana goyon matakan gurfanar da wadanda suka yi yinkurin juyin mulki a Turkiyya gaban shari'a, amma ya yi gargadin cewa kar gwamnati ta wuce makadi da rawa a yayin kokarin maido da doka da oda a kasar.

Ranar Lahadi Erdogan ya ce a shirye ya ke ya maido da hukuncin kisa a sanadiyyar yinkurin juyin mulkin. To amma babbar jam'iyyar harkokin kasashen waje na kungiyar Tarayyar Turai, EU, Federica Mogherini ta yi gargadin cewa daukar irin wannan matakin zai dakile fatan Turkiyya na zama mambar EU.