Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Saki Tsohuwar Matar Wanda Ya Tattake Mutane Kusan 300 A Faransa


A jiya Lahadi ne ‘yan Sandan Faransa suka saki tsohuwar matar mutumin nan da yayi amfani da wata babbar mota, wajen tattake mutane kusan 300 a birnnin Nice, amma har yanzu ana yiwa wasu mutane 6 tambayoyi domin tabbatar da cewa maharin shi kadai ne.

An kame mahaifiyar ‘ya‘yan Mohammed Lahouaiej Bouhlel uku ranar Juma’a. an kuma rike ta na tsawon wasu sa’o’i bayan da Bouhlel ya tuko katuwar mota da tafiyar tsawon kilomita 90 zuwa cikin birnin Nice, inda ya kashe mutane 84.

Lauyan matar ya fadawa gidan talabijin na Faransa cewa, bata da wata alaka da shi, bayan da ta kore shi daga gidanta lokacin da ya doketa.

Jami’ai sunyi imanin cewa Bouhlel ya aika da sakon karta kwana na wayar hannu minti 18 kafin ya kai harin, yana cewa “ka kawo ‘karin makamai, ka kawo guda biyar zuwa C,” har yanzu dai ba a san mai yake nufi da harafin C ba.

Cikin mutane shida dake hannun hukuma akwai mutumin da ake tunanin shi ne aka aikawa sakon karta kwanan, da kuma wata mace, baki daya dai an kama su ranar Lahadi.

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG