Fadar White House tace shugaba Obama ya yi magana ta waya da shugabar Jamus Angela Mikel a kan wannan abu, inda kuma su biyun suka amince da da cewa Rasha da gwamnatin Shugaba Assad suna da wani alhakin na musamman na dakatar da wannan yaki don bada daman shiga da kayan agaji ga mabukata.
Tuni da farko, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya fada jiya Alhamis cewa Amurka tana gab da janyewa tisnke tattaunawar diplomasiyya da take yi da Rasha saboda yanda Rasha din take ci gaba da ruwan bama-bamai a kan ‘yan tawayen dake gabashin Aleppo.
Dubban daruruwar fararen hula ne suka makale a wurin wanda rabinsu kananan yara ne.
Amurka dai tana kokarin yin matsin lamba ne akan Rasha don ita kuma ta matsawa kawarta, Syria, cewa ta girmama yarjejeniyar sulhun da aka kulla, kuma ta bar ayarin motocin MDD dake dauke da kayan agaji, su samu su shiga cikin garin na Aleppo.