A yau Laraba Amurka ta umarci ma'aikatanta da ba na gaggawa ba, da su bar kasar Iraki, matakin da aka dauka bayan da gwamnatin Trump ta yi gargadi kan yiwuwar sojojin Amurka da ke Gabas Ta Tsakiya zasu fuskanci barazana daga Iran ko kuma 'yan korenta.
Wata sanarwar da Ofishin Jakadancin Amurka na Bagadaza ya bayar, na cewa, wannan umurnin ya shafi ma'aikatan da ke wurin, da kuma wadanda ke karamin Ofishin Jakadancin Amurka da ke Irbil.
Shugaban Amurka, Donald, ya yi watsi da rahoton da ke cewa, yana tunanin aikawa da sojojin Amurka 120,000 don taka ma Iran burki, amma bai kau da yiwuwar tura abin da ya kira, "sojoji masu yawa" nan gaba ba.
"Ina tsammanin wannan labarin karya ne," abin da Trump ya fada kenan game da labarin da jaridar New York Times ta wallafa na cewa Fadar White House tana tunanin shirin tura sojojin Amurka 120,000 zuwa yankin.
"Shin, zai yiwu in yi haka? Shakka babu. To amma ba mu shirya yin hakan ba," a cewar Trump.