Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Shiryawa Musulmi Bude-Baki a Fadarsa


Walimar Iftar a fadar shugaban kasar Amurka, Donald Trump
Walimar Iftar a fadar shugaban kasar Amurka, Donald Trump

Shugaban Gasar Amurka Donald Trump ya yi jawabi na hadin kai a fadarsa, a lokacin da ya shirya walimar bude-baki ga jami'an diplomasiyyar kasashen da Musulmi suka fi rinjaye.

Shugaban Amurka Donald Trump ya shirya wa jami'an diflomasiyyar kasashen da Musulmi suka fi rinjaye bude-baki a fadarsa ta White House.

Trump ya kwatanta liyafar wacce aka yi jiya Litinin a matsayin, “babbar karramawa gare shi” ta shirya bude-baki ga jakadun kasashen duniya da Musulmai sukafi yawa.

Ya bayyana watan Ramadana a matsayin lokacin jin- kai ga marasa karfi, kyautata danganta da kara kusantar iyalai da jama’a.

Trump ya yi magana akan abin da ya kira “matsananancin lokaci” musamman ga mabiya wasu addinai, har ya tabo zancen wasu hare-haren da aka kai kan cibiyoyin addinai na Musulmai, Kiristoci da Yahudawa a kasashen New Zealand, Sri Lanka da nan Amurka.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra’ayoyin Amurkawa Kan Matsayar Trump, Harris Ga Mallakar Bindiga
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yaki Da Matsalar Almajiranci A Nasarawa
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:01 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG