Zaman tattaunawar da ake yi yau Laraba da wanda za a yi gobe Alhamis a Astana babban birnin Kazakhstan akan yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria, da Rasha ta dauki nauyi zata hada da wani jigon Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka da zai halarci zaman a matsayin dan kallo.
An tabbatar da hakan ne daga Fadar White House a wani rubutaccen bayani da ya biyo bayan tattaunawar wayar tarho da aka yi tsakanin Shugabn kasar Amurka Donald Trump da kuma takwaransa na Rasha Vladmir Putin.
Fadar White House ta bayyana kiran wayar na jiya Talata a matsayin “Mai kyau” an kuma tabbatar da ita ce magana ta farko ta kai-tsaye da aka yi tsakanin shuwagabannin guda biyu tun bayan da jiragen ruwan yakin Amurka suka kai hari da makamai masu linzami kan filin jirgin saman soji a Syria, wanda dakarun Syria da na Rasha suka yi amfani da shi a ranar 4 ga watan Afrilun wannan shekarar.
Trump ya alakanta Harin na makamai masu linzami da Amurka ta kai, wanda ya bata wa Rasha rai, da cewar ya faru ne sakamakon harin guba da Syria ta kai wanda yayi sanadiyyar mutuwar kimanin fararen hula 100.