Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar ISIS Ta Kai Hari Wani Sansanin 'Yan Gudun Hijra a Siriya


Farar hula akalla 32 ne su ka mutu jiya Talata a wani harin ba-zata da ISIS ta kai daura da wani sansanin 'yan gudun hijira a Siriya a kusa da kan iyakar Iraki, a cewar wasu da abin ya shafa da kuma jami'an Kurdawan Siriya.

An kai harin ne da asuba a yankin Rajm al-Saliben, wanda tamkar iyaka ce tsakanin mayakan ISIS da sojojin gamayyar da ke karkashin jagorancin Amurka, inda 'yan Siriya da Iraki da ke tserewa daga yankunan ISIS kan taru kafin a barsu su shiga yankin da ke karkashin ikon Kurdawa a arewacin Siriya.

Mayakan ISIS da dama bisa kan babura da motoci sun dumfari iyalai 300 masu gudun hijira daga Mosul na kasar Iraki da kuma Deir Ezzor na kasar Siriya su na jira cikin wasu tantuna da daren a wasu wuraren yada zango akan hanyarsu ta zuwa sansanin 'yan gudun hijira na al-Houl.

Fouad Omar, wani jami'i ba-Kurde daga Qamishili, ya gaya ma Muryar Amurka cewa mayakan na ISIS sun kuma daba ma 'yan gudun hijira wukake sannan su ka bude masu wuta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG