Ma’aikatar Cikin gidan kasar Afghanistan ta ce wani dan kunar bakin wake ya tayar da bom a yau Laraba, a yayin da jama’a ke hada-hadar fita aiki a birnin Kabul, harin da yayi sanadiyyar mutuwar kimanin mutane 8 ya kuma jikkata fiye da 25.
Mai Magana da yawun Dakarun rundunar NATO da Amurka ke jagoranta, Kyaftin Bill Salvin ya tabbatar da kai harin a kan daya daga cikin tankunansu na yaki. Ya kara da cewa uku da ga cikin sojojinsu na cikin wadanda suka jikkata amma raunukan da suka samu ba masu barazana bane ga rayuwar su.
Wadanda suka shaida lamarin sun ce fashewar bom din ya faru ne a kusa da ofishin jakadancin Amurka, haka kuma ya lalata motocin fararen hula da ke kusa, sannan mafiya yawan wadanda harin ya shafa duk fararen hula ne ‘yan kasar Afghanistan.
Tuni dai kungiyar IS ta dauki alhakin kai harin.
Facebook Forum