Amurka Ta Tsara Matakan Tinkarar Koriya Ta Arewa

Trump

Gwamnatin Trump ta tsara tsauraran matakan tinkarar Koriya Ta Arewa cikin ‘yan kwanakin nan, ta na mai cewa ita fa ta gaji ta take-taken Koriya Ta Arewar, a famar da aka dade ana yi ta tsai da niyyar Koriya Ta Arewa ta kirkiro makamin nukiliya.

“Ba za mu huta ba, ba kuma za mu hakura ba har sai mun cimma burinmu na kawar da nukiliya a yankin ruwayen Koriya,” a cewar Mataimakin Shugaban Kasa Mike Pence a birnin Tokyo jiya. Tun farko yayin da ya yada yango a birnin Seoul na Koriya Ta Kudu y ace, “Zamanin bi a hankali ya fa wuce,” inda ya ke nuni da salon gwamnatin Obama na taka tsantsan a matsayin wata dabara.


Ziyarar da Pence ya kai Arewa Maso Gabashin Asiya ta zo a daidai lokacin da Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro, Laftana-Janar Herbert Raymond MacMaster ya gaya ma kafar labaran ABC News cewa, “Mu na iya daukar kowane irin mataki” a Koriya Ta Arewa. To saidai duk da haka MacMaster ya bayyana fatan ba za a kai ga daukar matakin soji kan Koriya Ta Arewa ba.

A wasu tagwayen sakonnin twitter na kwanan nan Shugaba Trump ya bayyana Koriya Ta Arewa da wata “fitina” mai ‘neman tayar da masifa.’ Sannan sai ya cacci manufar Obama ta wajen rubuta cewa, “Sakamakon kwanaki 90 na farko a shugabanci na, ya fallasa gagarumar gazawar manufofin waje na shekaru 8 da su ka gabata.”