WASHINGTON DC —
Shugaban Amurka Donald Trump, yace kare rayuka "shine babban abunda yafi baiwa matukar muhaimmanci" yayinda mahaukaciyar guguwa da ruwan sama da aka yiwa lakabin "Florence ta auna yanki dake gabar teku mai fadin kilomita 40 a kudu maso gabashin Amurka.
"A shirye muke. Kuma zamu tunkare ta," shugaba Trump ya fada jiya Laraba.
Shugaban yace yayi magana da gwamnonin jihohin Carolina ta kudu data arewa, jihohi biyu dake kan hanyar da guguwar zata rasha.
Masana yanayi a cibiyar kula da iska masu tsanani ta Amurka suna gargadin Florence zata janyo ruwan sama mai yawan sentimita 101 a wasu sassan jihar Carolina ta arewa, inda ruwan teku zai tashi da tsawon mita hudu, fiyeda tsawon wasu gidaje.