Amurka Ta Saki Wani Makeken Bam a Afghanistan

Bam din da Amurka ta sake a Afghanistan mai suna GBU-43 MOAB,

Dakarun Amurkan sun ce sun saki wani makeken bam da ba na nukiliya ba akan wani gida dake karkashin kasa a Afghanistan.

Wata sanarwa da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta fitar, ta nuna cewa an saki bam din kirar GBU-43 ne a yau Alhamis a wata mabuya ko bututu na karkashin kasa a Gundumar Achin a Lardin Nangarhar dake kusa da kan iyakar Pakistan.

Wannan makami wanda aka fi sani da MOAB a takaice, na dauke ne da jerin bama-bamai a cikinsa da nauyinsu ya kai tan 11.

Saboda takaitaccen sunansa na MOAB na turanci da aka ba shi, dakarun saman Amurka sukan yi mai lakabi da “Mother of All Bombs” a turance – wato bam din da ya fi kowa ne nau’in bam karfi.

Kakakin ma’aikatar ta Pentagon, Adam Stump ya ce a wannan karo ne kawai aka fara amfani da wannan nau’in bam a fagen yaki.

Yayin taron manema labarai a yau, Kakakin Fadar White House, Sean Spicer, ya fada wa manema labarai cewa ba shi da masaniya ko shugaba Donald Trump ne ya ba da umurnin kai wannan hari.

Amma Spicer ya ce akwai bukatar a hana ‘yan kungiyar ta IS samun sakat, “kuma abin da muka yi kenan.” in ji Spicer.