Shirin makaman nukiliya na Korea ta Arewa da kuma katsalandan din Rasha a harakokin kasashen dake makwaptaka da ita da wadanda suke nesa da ita na cikin abubuwan da suka dauke hankulan kasashen.
Za’a ci gaba da kokarin tinkarar wadannan batuwa a wannan mako yayinda sakataren harkokin wajen Amurka Rex Tillerson ke haramar ganawa da takwarorinsa na kasashen duniya masu arzikin masana’antu na G-7 a Italiya kafin ya yi bulaguro zuwa birnin Moscow, babban birnin Rasha.
Sai dai kuma ana sa ran cewa za’a dada samun kwakkwaran sakamako daga taron kasashen na G-7 ya zuwa karshen watan Mayu lokacin da zasu yi taron kolinsu a Italiya.
Zaman tattaunawa tsakanin ministocin harkokin kasashen waje da ake gudanarwa yau Litinin zuwa gobe Talata, zai yi shimfida a kan tattaunawa da shugabanin kasashen zasu yi kafin lokacin da zasu hadu bai daya su tinkari maganar yadda za’a ga bayan kungiyar ISIS daga Syria da Iraqi.
Sakatare Tillerson ya fada a jiya Lahadi cewar Amurka na ci gaba da bada muhimmanci ga yarjejeniyar kawo karshen yakin Syria da aka kulla a Geneva a shekarar 2012, wanda a waccan lokacin yakin bai fi shekara guda ba kuma tuni ya zama babban kalubale ga bukatun jama’a.
Yarjejeniyar ta Geneva ta yi kira ne ga shirya sabon kundin tsarin mulkin Syria da gudanar da zabe, sai dai bata ce “kala” ba kan yanda za a yi da shugaba Bashar al-Assad ba.
Facebook Forum