Amurka Ta Saka Tukwicin Dala Miliyan $20 Ga Wanda Ya Ba Da Bayanan Wani Dan Iran Da Ake Zargi Da Yunkurin Kashe Bolton

Ma'aikatar Shari'a a Amurka

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Trump mai shekaru 78, wanda ke neman sabon wa’adin mulki a Fadar White House, ya yi ikirarin cewa Iran na barazana da rayuwarsa.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta sanar da tukwicin dala miliyan 20 a ranar Alhamis ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama wani dan Iran da ake zargi da hannu wajen yunkurin kashe tsohon jami’in Fadar White House John Bolton.

Jami’an Amurka sun ce a watan Agustan 2022 sun gano wata makarkashiyar da Shahran Poursafi, mamba a Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC), don kashe Bolton, wanda ya yi aiki a matsayi mai ba tsohon shugaban kasa Donald Trump shawara akan harkokin tsaro.

Shirin ba da tukwicin na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, “zai bayar da tukwicin dala miliyan $20 ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga kama Poursafi ko yanke masa hukunci, a cewar wata sanarwa da aka fitar a ranar Alhamis.

Matakin na zuwa ne a daidai lokacin da Trump mai shekaru 78, wanda ke neman sabon wa’adin mulki a Fadar White House, ya yi ikirarin cewa Iran na barazana da rayuwarsa.