Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dokokin Amurka Ta Kauce wa Rufe Ma'aikatun Gwamnati


Ginin Majalisar Dokokin Amurka
Ginin Majalisar Dokokin Amurka

Kakakin majalisa Mike Johnson kuma dan jam’iyyar Republican ya ayyana wannan matakin a matsayin, “wani abin da ya zama wajibi da babu makawa.”

Majalisar Dattijai ta amince da wannan matakin da kuri’u 78 da 18 jim kadan bayan da majalisar wakilai ta amince da kudurin.

Kudurin dokar zai ba da damar sahalewa hukumomin gwamnati kashe kudaden da suka saba kashewa yanzu zuwa 20 ga watan Diszamba.

Sai dai kuma, an kara wasu dala miliyan $231 da zimmar tallafawa hukumar tsaron farin kaya bayan yunkurin kashe dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Republican Donald Trump sau biyu.

Yanzu kuma za a kai wannan kudurin dokar kan teburin shugaban kasa Joe Biden don ya rattaba hannu akai a matsayin doka.

“Wannan hadin kan tsakanin duk jam’iyyu biyun, ya yi wa Amurka rana,” a cewar shugaban Sanatoci masu rinjaye Chuck Scumer jim kadan bayan kada kuri’a.

Ya kara da cewa “Ina fatan zai share fagen samun fahimta, tattaunawa mai ma’ana tsakanin jam’iyyun biyu a lokacin da zamu dawo a lokacin hunturu.”

Kakakin majalisa Mike Johnson kuma dan jam’iyyar Republican ya ayyana wannan matakin a matsayin, “wani abin da ya zama wajibi kuma babu makawa” kalaman da ya furta don ya isarwa wadanda suke nuna damuwa akan yawan kudaden da ake kashewa.

Ya zuwa yanzu dai, wasu ‘yan Republican ba su yi na’am da wannan matakin ba, lamarin da ya tursasa wa shugabannin daddadiyar jam’iyyar Republican da aka fi sani da GOP su yi dogaro da zaben ‘yan jam’iyyar Democrats da ya kai ga dokar ta samu nasarar amincewa da ita a wani tsari da ke bukatar kaso biyu cikin uku na kuri’un ‘yan majalisar.

Johnson ya ce abu daya da zai iya zama madadin sakamakon da aka cimma a wannan mataki shi ne rufe hukumomin gwamnati.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG