Amurka ta dauki mataki a hukumance a jiya Laraba na ficewa daga wata dadaddiyar kungiyar kasa da kasa, a wani yunkurin rage tsadar farashin aikawa da kananan kaya kasashen waje a Amurka.
WASHINGTON D.C. —
Wasikar sanar da ficewar Amurka a hukumance da ma’aikatar harkokin wajen Amurkan ta aikewa kungiyar da ake kira "Universal Postal Union" ko kuma (UPU) a takaice, martani ne a kan abin da gwamnatin Trump ta dauka a matsayin rashin adalci da China ke amfana sosai da shi da ma wasu kasashe kamar Faransa da Jamus da suke cin irin wannan amfani ta kasuwancin yanar gizo.
Bisa tsarin aikewa da kaya na kasa da kasa da ake amfani da shi a yanzu, aike kaya daga China zuwa Amurka yana da arha fiye da daga Amurka zuwa China din.
Bisa ga cewar wani jami'in Amurka, kasar China tana amfani da farashin aika sakonnin na kasa da kasa wajen saida kayayyaki na jabu da kuma miyagun kwayoyi kamar fentanyl mai sa maye zuwa nan Amurka.