Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ba-Amurken Nan Da Turkiya Ta Sake Daga Gidan Yari Ya Godewa Trump


Pastor Andrew Brunson da Trump
Pastor Andrew Brunson da Trump

Faston nan ba-Amurke da kasar Turkiya ta sake shi bayan ya yi zaman gidan yari tsawon shekaru biyu, ya gurfana a gaban shugaban Amurka Donald Trump a ofishinsa na Oval Office a fadar White House a jiya Asabar kuma ya yiwa shugaba Trump addu’a Allah kara masa hikima.

Andrew Brunson mallamin addinin Krista, ya kuma bayyana matukar farin cikinsa ga matsin lambar da gwamnatin Amurka ta yiwa Trukiya har ta samu nasarar kwato shi.

Brunson tare da iyalansa a ofishin shugaban kasar yace suna godewa wannan gwamnati, suka ce lallai an yi musu yaki.

Trump yace mutum ya fito gidan yari a Turkiya tsakanin sa’o’I 24 ya tsinci kansa a cikin White House, lallai babban abu ne.

Trump ya godewa shugaban Turkiya, Racep Tayyip Erdogan a kan sake Brunson, yana mai cewar babu wani kudin fansa da aka biya.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG