Kashoogi wanda rubuce rubucensa ke sukar lamirin yarima Mohammed bin Salman, ya bace tun lokacin da ya shiga cikin ginin ofishin jakadancin Saudiya a birnin Istanbul a ranar biyu ga wannan watan Oktoba.
Yace yakamata ya zuwa yanzu mun san abin dake faruwa. Yace da farko zaton mu kenan, saboda mun zaci ba a kashe shi ba, amma tana yiwuwa abu ya bace, saboda irin abubuwa da muke ji, inji Trump yana fadawa manema labarai a fadar White House.
Shugaban na Amurka Donald Trump ya yi kashedi cewa akwai jan kunne mai radadi ga Saudi Arabia idan har aka tabbatar da an kashe dan jaridar Saudi Arabia a cikin ofishin jakadancin ita Saudiyar a Istanbul a kasar Turkiya.
Facebook Forum