Amurka Ta Fara Jigilar Na'urorin Tarwatsa Makamai Masu Linzami

A dai dai lokacin da ake kara zaman dardar game da batun shirin nukiliya da makamai masu linzamai na Koriya Ta Arewa, yanzu haka Amurka ta fara 'daukar mataki.

Jiya Laraba sojojin Amurka sun fara jigilar wasu na'urorin tarwatsa makamai masu linzami sanfurin THAAD zuwa inda za a girke su a Koriya Ta Kudu, a cewar Koriya Ta Kudun.

"Koriya Ta Kudu da Amurka sun yi ta aikin tabbatar da ganin sun girke makamai sanfurin THAAD cikin lokaci, a matsayin martani ga barazanar nukiliya da makamai masu linzami da mu ke fuskanta dsaga Koriya Ta Arewa," a cewar Ma'aikatar Tsaron Koriya Ta Kudu a wata takardar bayani.

Tun a farkon watan Maris aka aika ma Koriya Ta Kudu wasu sassan makaman na THAAD.