Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Korea ta Arewa Ta Yi Bikin Tunawa Da Kafuwar Rundunar Sojojinta


Taron tunawa da kafuwar dakarun kasar Korea ta Arewa
Taron tunawa da kafuwar dakarun kasar Korea ta Arewa

Korea  ta Arewa ta yi  bikin cika shekaru  85 da kafa rundunar sojojin kasar, bikin wanda  take yi  yau,  ya na cike da wasan wuta, a gabashin tashar jirgin ruwan dake birnin Wonsan, in ji ma'aikatar tsaron Koriya ta kudu.

Masu kula da al’amurran ya da gobe, suna sa ran cewa kasar mai fasahar makamin nukiliya ta yi bikin tare da gwajin makamin ta na nukiliya zagaye na 6,ko kuma gwajin makami mai linzami amma ba dayan biyun da ta yi ya zuwa yammacin yau.

Wannan bikin yana zuwa ne daidai da ranar da jirgin yakin ruwan kasar Amurka ya isa Koriya ta kudu, yayin da jami'an sojan ruwan kasashen biyu sun hadu da kasar Japan domin gudanar da atisaye a cikin ruwan dake kudancin yankin Korea.

Atisayen na jami'an sojojin ruwan zai kai har zuwa gobe laraba, rana guda da shugaba Donald Trump ya gayyaci daukacin sanatoci su 100 Fadar White House domin tattaunawa akan batun Korea ta Arewa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG