"Sun jibga mana kayansu a nan Amurka," a cewar Trump, wanda ya kara da cewa, "Mutane sun kasa gane cewa Canada ta jima ta na kwarar Amurka... sun yi shekara da shekaru su na wayo ma 'yan siyasarmu."
Trump ya kara da cewa ya na so a labta ma katako da madarar Canada haraji.
Ya yi wannan kalamin ne a wata ganawa da manoman Amurka, inda ya yi amfani da ikonsa na Shugaban kasa wajen rattaba hannu kan umurnin da ya bayar kan bangaren noma da kuma yankunan karkara.
Trump ya kuma yi magana da Firaministan Canada Justin Trudeau jiya Talata. "Shugaba Trudeau yayi watsi da zarge-zargen nan marsa tushe da Ma'aikatar Cinakayyar Amurka ta yi da kuma matakin rashin adalci da aka dauka na saka haraji," a cewar bayanin Fadar Shugaban na Canda.
Facebook Forum