Wadanda zasu yi jawabi a wannan ganawar sun hada ne da Sakataren tsaron Jim Mattis da Sakataren harkokin waje Rex Tillerson da Darektan hukumar tattara bayanan sirri Dan Coats da kuma babban hasfin hafsoshi General Joe Dunford.
An saba yiwa ‘yan majalisar dattawan bayanai na musamman a majalisar ta Capitol Hill, ba kasafai ake musu irin wadannan bayanai a fadar White House ba ko kiran dukan bangarorin majalisar a lokaci guda.
A yayin wata liyafa da Jakadiyar Amurka a kwamitin sulhu na Majalisar dDinkin Duniya a jiya Litinin a fadar White House, shugaban Amurka ya kira halayen Korea ta Arewa da rashin cancanta.
Trump yace yakamata kwamitin sulhun MDD ya kakabawa shirin makamin nukiliyar Korea ta Arewa da makami mai lizzami kirar Balistic karin wasu takunkumai masu tsanani.
Korea ta Arewa babbban matsala ce ga duniya kuma matsala ce da yakamata mu maganceta baki daya, Mutane sun kau da idanu shekaru da dama, amma yanzu lokaci ya yi da za a yi magananin wannan matsa
Facebook Forum