Amurka Ta Fara Daukar Matakan Maida Martani Kan Koriya Ta Arewa

Jiragen saman yakin Amurka masu lugudan bama-bamai.

Jiragen saman yakin Amurka masu lugudan bama-bamai sunyi shawagi a saman ruwan Koriya, a wani mataki na mayar da martani kan gwajin makami mai linzami da Koriya ta Arewa ta yi.

Rundunar sojin saman Amurka ta yi shawagi da jiragenta masu ludugen bama-bamai samfurin B-1B bombers guda biyu, a sararin saman yankin ruwan Koriya a jiya Asabar, wadanda jiragen yakin Koriya ta Kudu da Japan samfurin jet su ka yi masu rakiya.

Rundunar sojin Amurka mai kula da yankin Pacific ta ce wannan matakin, wani martani ne na kai tsaye ga cigaba da kaddamar da makamai masu linzami masu tashi daga nahiya zuwa nahiya da Koriya Ta Arewar ta yi a ranakun 3 da 28 ga wannan wata na yuli.

"Koriya Ta Arewa na cigaba da kasancewa barzana mafi hadari ga kwanciyar hankalin yankin, " a cewar Janar Terrence O'Shaughaughnessy, Kwamandan sojojin Amurka a yankin na Pacific. "Har yanzu hanyar diflomasiyya ce ta fe, to amma kuma nauyi ya fa rataya a wuyanmu na kare kasarmu da kawayenta wajen nuna cewa ba fa da wasa mu ke yi ba, a yayin da kuma a lokaci guda mu ke ainihin shirn ko ta kwana. Muddun aka umurce mu to fa a shirye mu ke mu mai da martani a gaggauce, mai tsanani da kuma matukar karfi a duk lokaci da kuma wurin da ake bukata." a cewarsa.

Har ila yau dai a yau Asabar din, Shugaba Donald Trump na Amurka ya sake sukar kasar China saboda gazawarta wajen shawo kan Koriya Ta Arewa game da shirnta na makamai masu linzami da kuma nukiliya.