Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaba Trump Ya Canza Shugaban Ma'aikata A Fadar White House; Reince Priebus.


Shugaban ma'aikata Reince Priebus, wanda yayi murabus.
Shugaban ma'aikata Reince Priebus, wanda yayi murabus.

Sabon shugaban ma'aikatan shine Janar John Kelly,wanda kamin nadinsa shine ministan ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurka.

Shugaban Amurka Donald Trump, ya canza shugaban ma'aikata a fadar White, Reince Priebus. Wanda ya maye gurbin shine Janar John Kelly mai ritaya, wanda kamin wannan canji, shine ministan ma'aikatar tsaron cikin gida ta Amurka.
A makonnin baya bayan nan dai shugaba Donald Trump yana maida Priebus tamkar saniyar ware, ta kai ga sabon Darektan yada Labarai a fadar White House Anthony Scrammuci, ya ambaci Priebus din a zaman mutum "wanda yake da tabuwa".
Da take magana da manema labarai a maraicen Jumma'a, sakatariyar yada Labarai a fadar White House, Sarah Huchabee Sanders, tace "tun mako biyu da suka wuce ne, shugaba Trump da Reince Priebus, suka fara tattaunawa kan wannan canji".
A hira da yayi da tashar talabijin ta CNN bayan da yayi murabus, Priebus yace, "shugaban na Amurka yana so ya kawo canji."
" Ina ji lokaci yayi domin sauya fasali," in ji Priebus. Abu ne da a ganina fadar ta White take bukata."
Priebus yace gaskiyar magana, tun ranar Alhamis ya mika takardar sa ta murabus, amma sai jumma'a, aka bayyana ta.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG