Sama da mutane dari biyar maza da mata da kananan yara suka nemi kutsawa ta kan iyakar, suka bankade shingayen kan iyaka da ‘yan sandan kasar Mexico suka kakkafa, abin da yasa jami’an tsaron kan iyaka na Amurka suka harba barkonon tsohuwa, yayin da jiragen aikin tsaron kan iyaka masu saukar angulu suka rika shawagi a wurin.
Sakatariyar harkokin tsaron cikin gida Kirstjen Nielsen ta fada a wata sanarwa cewa, an rufe hanyar kan iyakar bisa dalilan tsaro, sakamakon yawan ‘yan ci ranin dake kokarin shiga Amurka ta barauniyar hanya.
Kamfanin dillacin labaran Reuters ya ambaci sanarwar ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar Mexico cewa, zata tasa keyar ‘yan ci rani dari biyar da suka yi kokarin ketara kan iyakar karfi da yaji. Sanarwar ta kuma kara da cewa, Mexico ba zata tura jami’an soji su sawa ‘yan ci ranin ido ba.