Dr. Abdullahi Wase masani akan harkokin tsaro yace kafin sanarwar da Najeriya ta fitar Amurka ta riga ta dakatar da sayen man Najeriya.
Bayan Amurka ta hana sayen man Najeriya bata tsaya nan ba. Ta hana sayarwa gwamnatin Najeriya makamai hatta harsashi kuma ta umurni kasashen Faransa da Birtaniya su yi hakan.
Amurka ta dauki matakan ne domin tana ganin gwamnatin Najeriya nada sakaci akan tabarbarewar tsaro a kasar. Tana ma tunanen gwamnatin Najeriya din tana marawa tashin tashinar kasar baya. Amurka tayi kokari ta ja kunnen gwamnati amma taki ta ji. Tsohon jakadan Amurka kafin ya tashi yace dole kasar ta dauki wasu matakai idan kuma ta ki to kafin shekarar 2015 za'a samu mummunan sakamako. Yace idan ba'a son kasar ta wargaje to dole ne gwamnati tayi takastantsan.
Rashin ganin gwamnatin Najeriya tayi takatsantsan ya sa Amurka ta hana sayarwa kasar makamai da kuma daina sayen man Najeriya. Ban da haka Amurka tayi korafin cewa bata ga alamar za'a bari ta koyas da sojojin Najeriya yadda yakamata ba. Tun kafin sanarwar dakatar da shirin Amurka tayi watsi dashi.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.
Your browser doesn’t support HTML5