Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram Sun Kai Hare-hare a Yobe da Borno


Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.
Shugaban ‘yan kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau.

Wasu da ake zaton 'yan Boko Haram ne sun kai hare-hare a jihohin Yobe da Borno

Wasu da ake jin cewa 'yan kungiyar Boko Haram ne ta masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama sun kai hare-hare jahohin Yobe da Borno a jiya Litinin.

Shaidu a Maiduguri sun ce fashe-fashe guda biyu sun yi raga raga da wata kasuwa mai cukowar jama'a inda wasu mata 'yan kunar bakin wake suka hallaka dimbin mutane a majkon da ya gabata. Shaidu sun ce mutane biyar a kalla ne suka mutu a harin na jiya Litinin. Shaidun suka ce sun ga mutane sun jike da jini, kuma wasu gabobin jikin su, sun guntule. Aka ce wasu mata biyu ne suka kai harin kunar bakin waken.

Kafin nan mazauna Damaturu babban birnin jahar Yobe sun ce 'yan Boko Haram sun kai harin kan jami'ar jahar da kuma wani ofishin 'yan sanda. Mazauna garin sun ce daliban jami'ar sun gudu sun shiga daji don su ceci rayukan su.

Sashen Hausa na Muryar Amurka yayi magana da wani dan jarida ma'aikacin gidan talbijin wanda shi ma a lokacin ya shiga daji kuma yana cewa 'yan bindigan sun isa tsakiyar birnin.

Kakakin ma'aikatar tsaron Najeriya Manjo-janar Chris Olukolade ya shaidawa manema labarai cewa sojojin da mayakan sama suka rufawa baya sun fafata a da 'yan tawayen a cikin Damaturu.

XS
SM
MD
LG