Da yake bayyana tallafin yau a Abuja, Jakadan Amurka a Najeriya, Ambassada Stuart Symington, ya ce karin tallafin na dala miliyan dari da biyu ($102 M) na aikace-aikacen jinkai ne a yankin arewa maso gabas inda za a samar da matsugunni, da kiwon lafiya, da abinci da kuma tsaro ga al'ummar yankin.
Wannan tallafi na daga cikin adadin dala miliyan dari da goma sha biyu ne da Amurka ta kebe don taimakon yankin Tafkin Chadi.
Amurka tace tana fata wannan karin taimakon ya zama silar yin aiki tare da gwamnatoci domin samun dauwamammen zaman lafiya da lumana a yankin,
Rikicin Boko Haram ya raba miliyoyin mutane da gidajensu a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Kuma kawo yanzu, Amurka ce ke kan gaba wajen bada tallafi.
Gwamnatin Amurka ta bai wa Najeriya taimakon dala miliyan dari da biyu domin a ci gaba da agazawa mutanen da rikicin Boko Haram ta rutsa da su a yankin Arewa maso gabas.
WASHINGTON DC —