Kakakin rundunar 'yan sandan Najeriya, ASP Moshood Jimoh ya yi wa manema labarai bayani kan inda aka kwana dangane da binciken alakar shugaban majalisar dattawan Najeriya, Dakta Bukola Saraki da kuma 'yan fashin da suka kashe mutane 33 ciki har da mata masu ciki da 'yan sanda 9.
Kakakin ya ce, suna da karin hujjar cewa 'yan fashin na da alaka na kut-da-kut da shi Saraki kamar yadda suka bayyana domin wani hoton da suka samu na daya daga cikin 'yan fashin, ya nuno shi sanye da ankon da 'yan uwa da abokan arziki suka saka a bikin diyar Sarakin. A saboda haka dole shugaban majalisar dattawan ya wanke kansa.
A ranar Litinin ne jagoran 'yan fashin ya bayyana cewa, su 'yan jagaliyar siyasar Saraki ne kuma baya ga su, akwai karin wasu manyan 'yan bindiga guda uku da ke aika-aika a sassa dabam-dabam na Jihar Kwara. Kakakin ya bayyana cewa su ma din an cafko biyu daga cikinsu.
"A sani cewa, har yanzu rundunar 'yan sandan Najeriya na binciken shugaban majalisar dattawa Najeriya, Bukola Saraki bisa zargin alaka da wadanda suka yi fashi a bankin Offa." inji Kakakin 'Yan sandan Najeriya.
'Yan sandan sun bukaci Saraki ya gabatar da kansa a ofishinsu wanda daga baya ya bayyana cewa rundunar ta shaida masa cewa ya wanke kansa a rubuce maimakon zuwa ofishinsu. Al'amarin da 'yan sanda suka musanta.
To in har yar hanzu gayyatar na nan kuma Dakta Saraki bai bayyana a gabansu ba, za su sa a kamo shi?
Kakakin ya amsa da cewa, "mai binciken ne zai iya tabbatar da haka."
Saurari cikakken rohoton Hassan Maina Kaina
Facebook Forum