Wasu daga cikin ‘yan majalisar Najeriya sun yi furucin da ya jawo hankalin majalisar wakilai saboda sun bayyana wa manema labarai rashin jin dadinsu da matakin da zaman taren majalisun biyu ya dauka akan shugaban kasa.
Akan hakan ne majalisar wakilai ta mika ‘ya’yanta biyu Abdulmummuni Jibrin da Muhammad Gudaji Kazaure ga kwaminta na bincike saboda sun yi zargin cewa taron majalisun biyu yunkuri ne na tsige shugaba Buhari. Sun kara da cewa tuni ma aka fara tara sunayen ‘yan majalisar dake da ra’ayin tsige shugaban.
Onarebul Lawal Yahaya Gumau ya yi tsokaci. A cewarsa idan ma Buhari ya yi wani laifi kamata ya yi kowace majalisa ta yi nata zaman kafin su zo su zauna tare su yi muhawara akan lamarin domin a samu matsaya. Ya ce duk wannan kai komon magana ce da ta shafi ‘yan sanda da shugaban majalisar dattawa.
A cewar Gumau ana son a yi anfani da majalisun biyu ne karfi da yaji, wato yin anfani da mutane dari hudu da ‘yan kai domin a goyi bayan shugaban majalisar dattawa. Wani yunkurin kuma shi ne a ce kota halin yaya akwai hannun Shugaba Buhari a matsalar da shugaban majalisar dattawa ke fuskanta da ‘yan sanda. Ya ce abun da suka sani shi ne babu ruwan Buhari da rikicin mutum da ‘yan sanda. Idan mutum nada Gaskiya babu yadda Shugaba Buhari zai ingiza ‘yan sanda su ci masa mutunci.
Gumau ya ce kowa nene ya karya doka cikin ‘yan majalisa ya fuskanci ‘yan sanda shi kadai.
Sanata Abdullahi Yahaya shi ma ya ce bai kamata a dauko lallurar wani ba ta zama ta majalisa. Wadanda aka kai kotu ba wannan gwamnatin ba ce ta kaisu. Barnar da suka yi ne tun lokacin gwamnatocin Obasanjo da ‘Yar’Adua amma kotunan ne basu yi aikinsu ba aka sake farfado da maganar yanzu. Duk wanda ake zarginshi da cin kudin jama’a ya je kotu ya kare kansa.
A saurari rahoton Medina Dauda da karin bayani
Facebook Forum