A yau Laraba Mr. Obama zai gabatar da jawabi a jami'ar AU dake nan birnin Washington DC. Shugaban yana shirin kwatanta jawabin da zai yi, da wani jawabin da tsohon shugaban Amurka John F. Kennedy, ya gabatar a makarantar, a shekarar 1963, inda shugaba
Kennedy yayi kira da Amurka ta gudanar da shawarwari ta hanyoyin difilomasiyya kan batun Nukiliya da tsohuwar tarayyar Soviet, mataki da ya kai ga rage gwaje gwajen, wanda daga karshe ya kai ga kulla yarjejeniyar hana gwaje gwajen baki daya a tsakanin kasashen duniya.
Majalisun dokokin Amurka suna cikin wa'adin kwanaki 60 suna nazarin yarjejeniyar, da suka ayyana jefa kuri'a akanta cikin watan Satumba, ko su amince da yarjejeniyar ko a'a. Shugaba Obama yayi alkawarin zai hau kujerar naki, mataki da zai tilastawa majalisun duka biyu su sami kashi biyu bisa ukun wakilan, wadanda basu amince da hawan kujerar naki da shugaban yayi ba,don tabbatar da cewa yarjejeniyar bata sami amincewar Amurka ba.