Amurka: Roof Ya Gurfana a Kotu Yau Kan Kasse Mutane Tara

Dylan Roof dan shekara 21 wanda ya kashe mutane tara

Dylan Roof dan shekara 21 wanda ya kashe mutane tara

A yau Juma’a ake sa rangurfanar da mutumin da ake zargi da kai hari kan wata Mijami’a a jihar South Corolina ta Amurka, a gaban kotu inda za’a yi batun beli, a kuma lokacin da jami’an tarayya suke ci gaba da binciken kisan gillar da ke da watakil ya aikata shi sabodanuna kiyayya.

Jami’an tsaron FBI ne suka dawo da matashin dan shekaru 21 mai suna Dylann Roof zuwa jihar South Corolina, daga jihar Carolina ta arewa, bayan daya kashe wasu mutane 9 alokacin da suke ibada, cikin su kuwa har da wata mata mai shekaru 87 da haihuwa, ya kuma raunata wasu mutane uku a wata Majami’a dake birnin Charleston ranar Laraba.

Yan sanda dai sunce Roof ya shiga cikin Majami’ar ne lokacin ibada kuma ya zauna yayi shiru har na tsawon awa guda, kafin ya mike yana cewa ya zame masa dole ya kashe bakar fata.

Wani ‘dan uwan daya daga cikin mutanen harin ya rutsa da su, ya gayawa gidan talabijin na CNN cewa ‘daya daga cikin mutanen da ya tsira ya gaya mata cewa kafin Roff ya fara harbi ya fadawa masu ibadar cewa, “Kun yiwa matan mu fyade, kun kwace mana kasa. Dole ne nayi abinda da ya kamata.”