Ministan tsaron Iran Hossein Dehqan ya fada jiya litinin cewa sabbin takunkuman da Amurka ke shirin sa wa Iran akan shirin mallakar makamai masu linzami ba zai yi wani tasiri ba akan sarrfa makaman.
WASHINGTON DC —
Shekaranjiya lahadi ne Amurka ta dauki sabbin matakan akan wasu ‘yan kasar Iran guda 5 da kuma wasu jerin kamfanoni da ke da alaka da hana ayyukan kera makamai masu linzami, matakin da ya biyo bayan dage takunkumin tattalin arzikin da aka sa wa shirin makaman nukiliyar Iran.
Dehqan ya kuma ce, takunkumin makamin mai linzami ya nuna cewa Amurka ba ta yarda da Iran ba kuma ya yi alkawalin fito da wasu sabbin shirye-shirye na makamai masu linzami kwanan nan.
Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Iran Hossein Jaber Ansari ya kira wadannan sabbin takunkuman a matsayin ba sa bisa doka.