Amurka Na Duba Alakar Maharan Texas Da IS

A lokacin da ake kawar da gawarwakin 'yan bindigar da suka kai hari a Texas

Hukumomi a Amurka na kokarin tantance ko akwai alaka tsakanin kungiyar IS da‘yan bindigan nan da suka kai hari a wajen wata gasa da wasu suka ce ta yin zanen Annabi Muhammad a jihar Texas.

Bayanai na cewa masu bincike suna duba shafukan Twitter na daya daga cikin mutanen da kuma kayayyakin wuta da maharan biyu suka yi amfani da su.

Kungiyar ta IS ta dauki alhakin harin, inda ta ce sojojinta biyu suka kai harin, wanda aka kai a Garland dake wajen birnin Dallas.

Kungiyar ta kuma ce wannan shi ne harin ta na farko a kasar ta Amurka, tana mai cewa mafi munin haka ma na tafe anan gaba.

Kakakin Fadar White House, Josh Earnest, ya ce gwamnatin Barack Obama ba za ta yi hanzarin bayyana cewa kungiyar ta IS ta shiga Amurka ba.

‘Yan sanda sun bayyana sunayen ‘yan bindigar a matsayin Elton Simpson da Nadir Soofi.

Mutanen biyu sun bude wuta ne akan jami’an tsaro a wurin gasar zanen, inda suka raunata wani jami’in tsaro, kafin daga baya wani dan sanda ya harbe su har lahira.

Musulmi a duk fadin duniya, na kallon yin zanen Annabi Muhammad, a matsayin wani babban zunubi.