Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurkawa da Ba Fararen Ba Zasu Dinga Fuskantar Babanci-inji Obama


Shugaba Obama tare da matasa
Shugaba Obama tare da matasa

Yayinda yake ganawa da matasan jisunan da ba farare ba Shugaba Obama ya fada cewa zasu dinga fuskantar wariya du da kokarin da gwamnati ke yi.

Shugaba Barack Obama ya fada jiya Littini cewa yan Amurka bakar fata da yan Latino sun yi karo da rashin sa’a domin wannan na daya daga cikin abinda yasa yan sanda ke nuna musu banbanci.

Shugaban yana magana a New York sailin da yake ganawa da tsirarun matasa. Yace matasa masu launin fata daban da na fararen Amurka na shan ukuba daga wurin yan sanda haka nan kawaibada wani dalili ba.

Yace wannan takurawar ceke haifar da tashe-tashen hankulla a birane irin su Baltimore, Fergason a Missouri.

Bayan kammala ganawar da wadannan matasan Mr Obama ya shaidawa manema labarai cewa abinda sukatattaunamusammam abinda suka ce abu ne dake da muhimmamci kwarai da gaske.

Shugaban yace duk da yake al’umma ba zata iya baiwa kowa tabbacin cewa zaiyi nasara a rayuwa ba amma akwai bukatar sama wa jamaa musammam matasa yanayin da zasu anfani rayuwar su.

Sai dai ya soki lamirin yan siyasa masu yawan batun samar da daidaito wajen samar wa kowa abinda yake bukata amma abinda suke fadi daban da abinda suke aikatawa.

An samu tashin hankali a garin Baltimore ranar Litini bayan da rahotanni suka bayyana cewa yan sanda sun harbi wani bakar fata da ake tuhuma da kokarin kaucewa kamu domin yana dauke da makamin da ya sabawa doka.

XS
SM
MD
LG