Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Taimakawa Kasashen Afirka da Miliyoyin Daloli


John Kerry Sakataren harkokin wajen Amurka yayinda yake jawabi a Nairobi Kenya jiya.
John Kerry Sakataren harkokin wajen Amurka yayinda yake jawabi a Nairobi Kenya jiya.

Sakataren harkokin wajen Amurka yace kasarsa zata karawa Kenya taimakon dala miliyan 45

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya fada jiya Littini a babban birnin Kenya- Nairobi cewa Amurka zata taimakawa kasashen Africa da miliyoyin daloli.

Kerry yace akwai karin dala miliyan 45 za’a asamar domin agaza wa yan gudun hijiran nan su dubu dari 6 da suke zaune a Kenya. Kerry ya yaba wa Kenya da daukar dawainiyar wadannan yan gudun hijiran.

Sai dai tun farko Kerry ya karrama wadanda harin bomb din nan na shekarar 1998 ya rutsa dasu a ofishin jakadancin Amurka dake Nairobi, dama wasu sauran hare-haren da kasar tayi fama dasu. Kuma yayi alkawarin cewa Amurka zata ci gaba da marawa kasar baya wajen yaki da ta’addanci.

Kerry yabi sahun shugabannin kasashen waje wurin bikin aza huren kallo a kabarin wadanda suka rasa rayukan su sakamakon harin bomb da aka kai a ofishin jakadancin Amurka. Yace har kullun yan ta’adda ba zasu yi nasara ba, duk ko da kokarin su ganin sun shuka tsoro ga zukatan mutane

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Malam Bello Abba Yakasai masani kan harkokin noma ya yi karin haske akan matsalar tsaro ga manoma da hanyoyin magance wannan matsala
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p

No media source currently available

0:00 0:04:20 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 810p
  • 720p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG