Amurka ta bukaci Isra’ila da ta kara fadada ayyukan jin-kai ga Fasladinawa da ke fama da yunwa a Gaza a cikin wata mai zuwa ko kuma ta fuskanci yiwuwar katse taimakon soji da take bai wa Isra’ila a yakin da ta shafe shekara guda tana yi da mayakan kungiyar Hamas.
Gargadin ya zo ne a ranar Lahadin da ta gabata a wata wasika da Washington ta aike wa jami’an Isra’ila tare da nuna matukar damuwa kan tabarbarewar ayyukan jin-kai a Gaza.
“Abin da muka gani a cikin ‘yan watannin da suka gabata shi ne, yanayin ayyukan jin-kai ba ya dorewa. A gaskiya, sun yi kasa da sama da kashi 50 cikin 100 daga inda yake a kololuwarsa a baya.” In ji Matthew Miller, Kakaki a Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.
Kalaman na Amurka na zuwa ne a daidai lokacin da Isra’ila ke ci gaba da kai hari kan mayakan Hezbollah a Lebanon da sabunta hare-haren da take kai wa kan Hamas a arewacin Gaza.
Tsawon watanni, duk da cewa fadan Isra’ila da Hamas na ci gaba, Amurka ta sha matsawa Isra’ila lamba da ta kara bari a shigar da kayayyakin agajin jin-kai cikin yankin, wadanda suka hada da abinci, ruwa, magunguna, man fetur da sauran kayayyaki zuwa ga fararen hula Falasdinawa.