Amurka da kasar Rasha na aiki kafada da kafada don samar da yarjejeniyar tsagaita wuta a Syria, wadda zata bayar da damar shigar da kayan jinkai kasar da yaki ya ‘dai ‘daita, yayin da shugabannin duniya suke haduwa a birnin Hangzhou na China, a taron kolin G-20.
WASHINGTON D.C —
Kasashen biyu na dab da cimma yarjejeniyar, amma har yanzu dai akwai kalubale. Ana fatan cewa shugaban Amurka Barack Obama da shugaban Rasha Vladimir Putin zasu samu damar ganawa da juna a taron kolin da ake gudanarwa na G-20. Amma har yanzu dai babu wani shiri kan hakan.
Anji shugaban Rasha Vlamir Putin, na cewa ta hanyar siyasa ne kawai za a iya warware rikicin Syria.
Kasar Rasha dai ta marawa shugaban Syria Bashar al-Assad baya, amma kuma Amurka na aiki da dakarun ‘yan tawayen da ke yakar Assad.
Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry ya gana da takwaransa na Rasha Sergei Lavrov a jiya Lahadi, yau Litini kuma zasu sake ganawa.